Kona Masallaci: Gwamnan Kano ya sha alwashin daukar mataki da yin adalci

Abba Kabir Yusuf, kona, masallaci, jihar, kano, mataki, adalci
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi alkawarin tabbatar da adalci ga wadanda harin da aka kai a wani masallaci a kauyen Gadan da ke karamar hukumar...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi alkawarin tabbatar da adalci ga wadanda harin da aka kai a wani masallaci a kauyen Gadan da ke karamar hukumar Gezawa a jihar.

Harin wanda ya rutsa da rayukan mutane 15, ana zargin Shafi’u Abubakar ne ya kai kan wata takaddama da ta shafi rabon gado.

Karin labari: ‘Yan bindiga sun sace mutum 16 yayin da ‘Yan sanda suka ceto mutum 4 a Abuja

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Yusuf ya yi magana ne a lokacin da ya ziyarci wadanda abin ya shafa a asibitin kwararru na Murtala Muhammad a ranar Litinin.

Abba ya yi Allah-wadai da harin, ya bayyana cewa gwamnatin jihar da jami’an tsaro za su bi diddigin lamarin har zuwa karshensa.

Karin labari: ‘Yan gwadago za su halarci taron tattaunawa a kan mafi karancin albashi

Gwamnan ya kara da cewa lamarin bai shafi ta’addanci ko rikicin siyasa ba, sai dai batun rikicin dangi da ya rikide zuwa tashin hankali.

Ya ce wanda ake zargin zai fuskanci fushin doka ta hanyar gurfanar da shi a gaban kotun Shari’a.

Idan aka same shi da laifi, gwamnan ya yi alkawarin rattaba hannu kan sammacin kisan wanda ake zargin, tare da tabbatar da tanade-tanaden doka kan shari’o’in kisan kai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here