Tinubu ya fara hutun kwanaki 10, ya bar Abuja zuwa Turai

Tinubu depart US 750x430

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara hutun kwanaki 10 a matsayin hutun sa na shekarar 2025 a yau Alhamis.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ta ce shugaban zai shafe kwanaki 10 yana hutun aiki tsakanin Faransa da Birtaniya, daga nan kuma zai dawo Najeriya.

Karin karatu: Tinubu ya naɗa Bunkure a matsayin shugaban Jami’ar Tarayya ta Zariya, ya naɗa Nakore da Kodage a majalisar gudanar a Jami’ar ilimi ta tarayya a Kano

Sanarwar ta ce, shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a yau 4 ga watan Satumba, domin fara hutun aiki a Turai, a wani bangare na hutun shekara ta 2025.

“Shugaba Tinubu zai shafe tsawon lokaci tsakanin Faransa da Birtaniya sannan ya dawo kasar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here