Majalisar Malamai Ta Sanar Da Lokacin Sallar Jana’izar Dantata, Wuri

WhatsApp Image 2025 06 28 at 06.37.29 720x430.jpeg

Majalisar Malamai ta Kano ta sanar da cewa za a gudanar da (Salatul Ga’ib) sallar jana’izar marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya rasu a jiya Juma’a.

A cewar sanarwar da shugaban majalisar Malam Ibrahim Khalil ya fitar, an shirya gudanar da sallar ne da misalin karfe 2:00 na rana a masallacin Umar Bin Khaddab da ke Gyadi-Gyadi a Kano.

Ya kuma tabbatar da wannan tsari tare da yin kira ga al’ummar Musulmi da su halarta da yi wa marigayin addu’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here