Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da NDC aKaramar Hukumar Bichi ta jihar.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Kano.
A cewarsa, rikicin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:45 na yammacin ranar Lahadi, inda aka lalata fastocin kamfen, allunan siyasa da motoci, tare da jikkata wasu mutane.
Ya ce jami’an ’yan sanda sun gaggauta isa wurin bayan samun rahoton faruwar lamarin, inda suka yi nasarar shawo kan rikicin tare da dawo da zaman lafiya.
Kiyawa ya bayyana cewa an lalata motoci 13 yayin rikicin, yayin da aka garzaya da mutane biyar da suka samu raunuka zuwa asibiti domin ba su kulawa.
Ya kara da cewa kayayyakin da ’yan sanda suka kwato sun haɗa da Gariyo guda ɗaya, adduna biyu, sanduna masu kaur biyu, kwalbar wani sinadari da kuma wani abu da aka fi sani da suna “Suck and Die”.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Bakori, yana Allah-wadai da rikicin da kuma lalata kayan kamfen da wasu magoya bayan siyasa suka yi.
Kwamishinan ya gargaɗi cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani abu da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma kafin lokacin siyasa, lokacin gudanar da zaɓe ko bayan zaɓe ba.
Ya kuma buƙaci shugabannin siyasa da magoya bayansu da su gudanar da harkokinsu cikin lumana tare da bin dokokin ƙasa.
Read also: Za’ayi Jana’izar Buhari A Daura Ranar Talata -Radda
Kakakin rundunar ya ce an miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin gudanar da bincike cikin sirri.












































