Wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka guda biyar sun gabatar da wani kudiri a Majalisar Wakilai domin tilasta wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka gabatar da cikakken rahoto kan kokarin Amurka na magance abin da suka kira tsanantawar addini da manyan laifuka a Najeriya.
Idan kudirin ya zama doka, ana sa ran Ma’aikatun Harkokin Waje da Baitulmali na Amurka za su kakaba takunkumi da suka hada da haramta biza da kuma daskarar da kadarori kan daidaikun mutane ko kungiyoyin da ake zargi da take hakkin ‘yancin addini a Najeriya.
Kungiyoyi da mutum daya da aka lissafo cikin wadanda za a kakaba wa takunkumin sun hada da tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, da kungiyar Fulani ta Miyetti Allah (MACBAN), da ita ma kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, da sauransu.
An gabatar da kudirin ne ranar Talata a Majalisar Wakilan Amurka, kuma ‘yan majalisar da suka dauki nauyin sa sun hada da Chris Smith, Riley Moore wanda shi ne marubucin kudirin, Brian Mast, Mario Diaz-Balart da Bill Huizenga.
Ƙudurin ya samu sunan Dokar ‘Yancin Addini da Taimakon Addinin Najeriya na 202, inda masu daukar nauyin sa suka ce Shugaban Amurka Donald Trump ya yi daidai da ya sake ayyana Najeriya a matsayin kasa mai matukar damuwa kan batun ‘yancin addini.
‘Yan majalisar sun bayyana cewa ya kamata Amurka ta yi amfani da dukkan hanyoyin diflomasiyya, jin kai, tattalin arziki da tsaro domin matsa wa gwamnatin Najeriya ta kawo karshen rashin hukunta masu aikata manyan laifuka da tsanantawar addini tare da kare al’ummomin Kiristoci da sauran tsirarun addinai.
Dangane da tanade-tanaden kudirin, ana sa ran Sakataren Harkokin Waje zai tantance ko wasu kungiyoyin Fulani a Najeriya sun cancanci a ayyana su a matsayin kungiyar ta’addanci ta kasashen waje, tare da kakaba takunkumi karkashin dokar Global Magnitsky Human Rights Accountability Act idan an same su da laifi.
Marubucin kudirin, Riley Moore, na daga cikin ‘yan siyasar Amurka da suka dade suna ikirarin cewa akwai tsanantawar Kiristoci a Najeriya, kuma ya ziyarci kasar a watan Nuwamba 2025 kan wannan batu.
A watan Nuwamba 2025, Trump ya ayyana Najeriya a matsayin kasa mai matukar damuwa, matakin da ke bai wa bangaren zartarwa na Amurka damar daukar matakan diflomasiyya da tattalin arziki, sannan ya kuma amince da hare-hare na hadin gwiwa da gwamnatin Najeriya kan wadanda ake zargi da ta’addanci a ranar Kirsimeti ta 2025.













































