Tinubu ya naɗa sabon Shugaban hukumar NAHCON

tinubu 2

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Darakta na Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON).

Naɗin nasa na cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.

Tun da fari Tinubu ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wasiƙa a yau, yana neman a gaggauta tantance Ambasada Yusuf domin ya maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a wannan mako bayan kusan watanni 14 a kan muƙamin.

Naɗin, wanda aka sanar a ranar Laraba, na buƙatar amincewar Majalisar Dattawa bisa tanadin sashe na 3(2) na Dokar NAHCON.

Yusuf ƙwararren jami’in diflomasiyya ne, kuma ya yi aiki a matsayin Jakadan Najeriya na Musamman kuma Mai Cikakken Iko a Jamhuriyar Türkiye daga 2021 zuwa 2024.

Murabus ɗin Usman a ranar Litinin, watanni 14 kacal bayan fara aikinsa, ya zo a wani lokaci mai muhimmanci ga hukumar, yayin da shirye-shiryen Hajjin 2026 suka riga suka fara.

NAHCON ita ce hukumar tarayya da ke da alhakin tsarawa da daidaita ayyukan Hajji da Umrah a Najeriya, ciki har da ba da lasisi ga masu shirya tafiya da kula da jin daɗin maniyyata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here