Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, ya bayar da umarnin gaggauta dakatar da Auwalu Danladi Sankara, Kwamishinan Harkoki na Musamman, bayan wasu zarge-zarge masu nauyi da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi masa.
Dakatarwar ta fito ne ta cikin wata sanarwa da Malam Bala Ibrahim, Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, ya rattaba hannu.
Ana zargin Sankara da yin mu’amala ta badala da wata matar aure, tare da wasu laifuka daban.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta tabbatar da kama Sankara a ranar Jumma’a, bayan sun bi diddigin ayyukansa.
A cewar Darakta Janar na Hukumar, Dakta Abba Sufi, an kama Sankara a cikin wani gini da ba a kammala ba tare da wata matar aure, bayan korafe-korafen da aka samu daga kanin mijin matar.
“Muna da tabbacin cewa mun kama Auwalu Danladi Sankara, Kwamishinan Jigawa, tare da wata matar aure a cikin wani gini da bai kammalu ba,” in ji Dakta Sufi ga manema labarai, yana mai cewa kamen yana cikin wani bincike mai zurfi kan halayen rashin da’ar Kwamishinan.
Mijin matar, Nasiru Bulama, ya shigar da korafi na hukuma ga ‘yan sanda, Hukumar Tsaro ta DSS, da kuma Hukumar Hisbah, yana zargin Kwamishinan da yin alaka ta asiri da matarsa, Tasleem Baba Nabegu, uwar ‘ya’yansa biyu.
Bugu da ƙari, ana zargin Sankara da yin harkalla da shaye-shaye a wasu wurare da ake kira Picklock da 360.
Gwamnatin Jihar Jigawa ta jaddada cewa dakatarwar mataki ne na kariya domin bayar da damar gudanar da bincike cikin adalci da gaskiya, tare da tabbatar da martabar gwamnati.
Gwamna Namadi ya jadda tabbatar da cikakken adalci da bin doka da oda a cikin shugabanci.
“Dakatarwar mataki ne na kariya da aka dauka domin bayar da damar gudanar da bincike na gaskiya,” in ji Bala Ibrahim, yana mai jaddada kudurin gwamnati na kare ka’ida da martabar jama’ar Jigawa.