Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta tsawaita wa’adin ɗaukar bayanai da rarraba maniyyatan Najeriya na aikin Hajjin 2026, bayan wata bukata ta gaggawa da gwamnatin Najeriya ta gabatar.
Matakin tsawaitawar ya biyo bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya umarci Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, da ya roƙi hukumomin Saudiyya.
Amincewar da suka yi na nufin masu kula da harkokin Hajji a Najeriya sun samu ƙarin lokaci domin kammala bayanan maniyyata.
Mataimakiyar Darakta ta Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), Fatima Sanda Usara, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta yi gargadin cewa wannan shi ne karo na ƙarshe na tsawaita wa’adin, tare da buƙatar hukumomin Hajji a faɗin Najeriya su yi aiki cikin ƙwazo da gaggawa domin kammala dukkan matakan ɗaukar bayanai don guje wa matsaloli na ƙarshe.
Wannan tsawaitawa ta zo ne kwana biyu bayan rufe dandalin ɗaukar bayanai na Nusuk Masar a duniya baki ɗaya.
NAHCON ta sake jaddada aniyarta na samar da ayyuka masu inganci da suka mayar da hankali kan jin daɗin maniyyata, tare da alƙawarin yin aiki tukuru domin nasarar Hajjin 2026.













































