Kwamitin kar-ta-kwana na Gwamnatin Jihar Kano kan Tashoshin Mota da Sauran Wuraren Jama’a ya kwace haramtattun magunguna, na jabu da kuma waɗanda wa’adin su suka ƙare da darajarsu ta haura Naira Biliyan 1.5 a kasuwar Dan-Gwauro da ke Karamar Hukumar Kumbotso.
SolaceBase ta ruwaito cewa matakin ya biyo bayan sanarwa daga shugabannin kasuwar da suka nuna shirinsu na mika magungunan da aka kwace ga gwamnati domin lalata su.
Sai dai kwamitin ya samu bayanai daga jami’an sa na sirri kan samuwar wasu haramtattun magunguna a kasuwar.
Saboda haka aka kai samame a daren Talata, inda mambobin kwamitin suka balle wani dakin ajiya da ke cikin ofishin kasuwar, suka gano dimbin haramtattun magungunan Hyxul da darajarsu ta haura Naira Biliyan 1.
Tun da farko, Shugaban kasuwar, Alhaji Husaini Labaran Zakari, ya mika wani rukuni na magungunan da aka kwace da kuma waɗanda suka ƙare.
Zakari ya ce wasu daga cikin magungunan hukumomin kasuwar ne suka kwace su, yayin da wasu kuma masu su suka mika da kansu.
Ya kara da cewa an sanar da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), kuma tana sa ido kan lamarin.
Yayin karbar kayayyakin, Shugaban Kwamitin, Manjo Adamu Abubakar Usman mai ritaya, ya ce yawan magungunan da aka kwace ya yi yawa domin sun cika tirela guda, kuma za a mika su ga gwamnatin jiha domin daukar matakin da ya dace,” in ji shi.
Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kafa kwamitin domin karfafa yaki da shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi a Kano, yana mai cewa matakin ya dace da manufar gwamnati ma kin jurewa haramtattun abubuwa.
Manjo Usman ya ce wasu daga cikin bayanan da suka kai ga samamen sun fito ne daga majiyoyin sirri, yayin da shugabannin kasuwar ma suka bayar da karin bayani.
Ya bukaci ‘yan kasuwa a fadin jihar su mara wa gwamnati baya ta hanyar bayar da sahihan bayanai domin yaki da yaduwar magunguna masu hadari da na jabu.
Daga bisani an loda magungunan a kan tirela tare da kai su Gidan Gwamnatin Jihar Kano domin ci gaba da da lalata su.













































