Rundunar sojojin ruwa ta kasa ta sanar da ranar da zata bude shafinta na yanar gizo domin daukar ma’aikata

navy 1
navy 1

Rundunar sojujin ruwa ta kasa ta ce ta shirya tsaf domin fara daukar ma’aikata, domin ta bunkasa harkokin tsaro a kasa baki daya.

Shugaban sashin yada labarai na rundunar, kwamanda Adedotun Ayo-Vaughan, shine ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, cewa za’a budin shafin rundunar na yanar gizo ranar Labara, domin ‘yan Najeriya su nema aikin.

Ya kara da cewa daukar ma’aikatan na daya daga cikin kokarin shugaban sojujin ruwa na kasa, Adm. Awwal Gambo, na bunkasa rundunar a fadin kasa baki daya.

“ za’a budi shafin ne ranar 7 ga watan Agusta, sanan za’a rufe 7 ga watan Satumba”

“ kyauta ake yin rigistar, kuma duk wanda ya nema sau biyu za’a zare sunan sa daga cikin wadan da suka nemi aikin”

“Dole ne duk wanda ya nema aikin ya tabbatar ya sami nasarar cin darusa 5 a jarrabawar WASSCE/SSCE/GCE/NECO/NABTEB, wanda suka hada da darasin Turanci da na Lissafi”

Shafin da za’a nemi aikin shine www.joinnigeriannavy.com

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here