Wani mummunan hatsarin mota da ya afku a yankin Kwanan Maciji da ke karamar hukumar Pankshin a jihar Filato a karshen mako ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 tare da jikkata wasu 11.
Wadanda lamarin ya rutsa da su sun taso ne daga jihar Kano domin halartar wani daurin aure a karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato, suna komawa gida ne a lokacin da hadarin ya afku a ranar Asabar.
Shugaban kwamitin bayar da agajin gaggawa na karamar hukumar Pankshin, John Dasar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai bayyana lamarin a matsayin mummunan lamari.
A cewarsa, wadanda abin ya shafa sun yanke shawarar bin hanyar Gindiri zuwa jihar Bauchi ne a lokacin da motarsu ta yi hatsari.