Ba a min laifi ba, na fita daga PDP ne dan kishin Arewa – Bafarawa

Screenshot 20250114 222204 Facebook

 

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya yi karin bayani game da dalilansa na fice wa daga jam’iyar PDP a yammacin yau Talata.

Bafarawa ya ce jam’iyyar PDP bata masa laifin komai ba, illa kawai ya fita ne domin kishin Arewa da kullum ta ke fuskantar koma baya.

Ya bayyana haka ne a yayin wata zantawa da wakilin Trust Radio a yau Talata.

A zantawar ta su, Bafarawa ya ce lokaci ya yi da dole su nema wa Arewa mafita, kuma ba shi kadai ba ne a wannan tafiya.

Ya kuma bayyana cewa sun kirkiri kungiya wadda bata da alaka da jam’iyyar siyasa domin samar da nagartattun shugabanni a yankin dama kasa baki daya.

“Mun yi kungiya wadda ta hada da Musulmi da kirista da yara (matasa) domin hadin kan Arewa.”

Ya kara da cewa idan lokacin zabe yayi, wannan kungiya za ta ke zabar shugaba daga cikin matasa ta kuma yi kira da al’uma su zabe shi.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here