Kotu ta ki amincewa da neman belin Abba Kyari, Ubua

Abba Kyari new 1
Abba Kyari new 1

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja karkashin jagorancin mai shari’a Emeka Nwite a ranar Litinin ta yi watsi da bukatar neman belin da mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar (DCP) Abba Kyari da DCP, Sunday J. Ubua.

Ana tuhumar su biyun ne da wasu biyar dangane da laifukan da suka shafi mu’amalar muggan kwayoyi ba bisa ka’ida ba.

Mai shari’a Nwite, a wani hukunci da ta yanke a safiyar ranar Litinin, ta ce masu gabatar da kara sun gabatar da isassun hujjoji a gaban kotu domin kin bada kin bayar da belin manyan jami’an ‘yan sanda biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here