Ministan Ilimi Dr. Maruf Olatunji Alausa, ya bayar da shawarar tsawaita shirin yi wa kasa hidima (NYSC) daga shekara daya zuwa biyu, tare da fadada abubuwan da suka kunsa na shirin Koyar da Sana’o’i da samar da harkokin kasuwanci ga mambobin hukumar.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Abuja.
A cewar wata sanarwa da hukumar ta NYSC ta wallafa a shafin sada zumunta na Facebook, Ministan ya kuma bayar da shawarar tura karin malaman da suka kammala karatu zuwa makarantun karkara, inda ya ce hakan zai cike gibin ma’aikata a makarantun.
Ya yabawa mahukuntan hukumar NYSC bisa himma da kuma na’urar tantance masu yi wa kasa hidima, da nufin dakile badakalar takardar shaidar da ta shafi wasu daliban da suka kammala karatun digiri a kasashen waje a yammacin Afirka.
Ya kuma yaba da shirin na magance matsalar da ta dabaibaye daliban da suka kammala karatun digiri na OND tare da cikakken lokaci da HND wadanda a baya an cire su daga aikin yi wa kasa hidima.
Farfesa Alausa ya ci gaba da cewa ana ci gaba da kokarin ma’aikatar wajen tantance wadanda suka kammala karatu daga kasashen waje ‘yan asalin Najeriya, inda ya ce ma’aikatar da NYSC za su kara karfafa hadin gwiwarsu na inganta ilimi domin ci gaban kasa.
Da yake jawabi tun farko, Darakta Janar na NYSC, Brig-Gen. Nafiu, ya yaba da sabbin tsare-tsare da kuma gagarumin ci gaban da Ma’aikatar ta samu a fannin ilimi.
Ya yi kira da a kafa ma’adanar bayanai na matasan Najeriya da ke fita kasashen waje domin yin karatun digiri, ya kara da cewa hakan zai taimaka wa gwamnati da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi wajen samun cikakken bayanan daliban Najeriya da ke karatu a kasashen waje da kuma kawar da jabun wadanda suka kammala karatun digiri.
Babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya, Mista Abel Olumuyiwa Enitan, ya tabbatar da shirin ma’aikatar na yin aiki tare da NYSC yadda ya kamata domin daga darajar ilimi a kasar nan.