Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ya sanar da sauye-sauye ga hukumarsa da manyan jami’anta, tare da sauke Umar Ajiya da Oritsemeyiwa Eyesan daga mukamansu na babban jami’in kudi.
A madadin su, NPL ta nada Isiyaku Abdullahi a matsayin sabon mataimakin shugaban zartarwa na Downstream da Udobong Ntia a matsayin EVC (Upstream).
Hakanan, Adedapo Segun, wanda ya kasance EVP (Downstream) an nada shi babban jami’in kudi.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta NNPC ta fitar a daren Larabar da ta gabata, ta ce nade-naden na da nufin inganta harkokin tafiyar da harkokin kamfanoni da kuma yadda ake gudanar da ayyuka, wanda hakan ke nuni da yadda kamfanin na NNPC ya jajirce wajen samun nasara na dogon lokaci a fannin makamashin Najeriya.