Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Attahiru Jega ya ce ya kamata a hana ma’aikatan gwamnati daukar mukaman gargajiya a lokacin da suke hidima domin dakile yawaitar ayyukan cin hanci da rashawa.
Jega ya yi wannan kiran ne a ranar Larabar da ta gabata a taron tattaunawa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta ICPC tare da manyan jami’an hukumomin gwamnati, kan hana cin hanci da rashawa a cikin ma’aikatan gwamnati a Abuja.
A cewarsa, wani abin zaburarwa ne ga mahukuntan gargajiya na ba da mukamai ga jami’an gwamnati.
Tsohon shugaban hukumar ta INEC ya ce, “daukar mukami na gargajiya na sa jami’in gwamnati ya zama mai saurin cin hanci da rashawa da kuma zagon kasa ga gudanar da mulki yayin da ya ke ba da damar matsa lamba kan yin hakan.