
Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya AMBCN, ta bayyana janye yajin aikin da ta shiga bayan wata tattaunawa da ta gudanar da jami’an ma’aikatar noma ta ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar Laraba, wadda ta samu sa hannun shugabanta Mansur Umar, ƙungiyar ta ce ta cimma wasu yarjeniyoyi da gwamnatin Najeriya a tattaunawar ta su, wanda hakan ya sanya ta sanar da janye yajin aikin wanda ta fara a ranar Talata.
Karin labari: Tinubu zai kai ziyara kasar Qatar don kasuwanci da zuba jari
Daga cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙungiyar da gwamnati sun haɗa da fitar da metric tan 25,000 na alkama nan take ga kamfanonin fulawa domin sarrafawa da samarwa masu sana’ar burodi.
Haka nan ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniya kan sake duba shirin samar da fulawa daga rogo da dankali da kuma dawa.
Karin labari: An sako wasu ‘yan Italiya 3 da aka yi garkuwa da su a 2022 a Mali
Sannan kuma an cimma yarjejeniyar tallafawa masu sana’ar ta burodi ƙarƙashin wani shiri na ma’aikatar noma ta Najeriyar.
Masu gidan burodin a Najeriya sun shiga yajin aiki ne bayan kokawa da tsadar farashin kayan aiki, lamarin da ke kawo tarnaƙi a harkar sana’ar tasu.
Najeriya na fama da tashin farashin kayan masarufi, lamarin da ake dangantawa da cire tallafin man fetur a ƙasar da kuma wanu manufofi na gwamnati.