An sako wasu ‘yan Italiya 3 da aka yi garkuwa da su a 2022 a Mali

'Yan bindiga, Italiya, garkuwa, mali
An sako wasu ‘yan ƙasar Italiya uku da aka yi garkuwa da su a Mali a watan Mayun 2022, kamar yadda wani gidan intanet na Bamako ya rawaito. Rahoton ya ce...

An sako wasu ‘yan ƙasar Italiya uku da aka yi garkuwa da su a Mali a watan Mayun 2022, kamar yadda wani gidan intanet na Bamako ya rawaito.

Rahoton ya ce “An sako Rocco Langone da matarsa ​​Maria Donata Caivano da ɗansu Giovanni Langone, ‘yan ƙasar Italiya da aka yi garkuwa da su a ranar 19 ga Mayun 2022 a kusa da Koutiala a kudancin Mali a daren ranar 26-27 ga watan Fabrairu.”

Rahoton ya bayyana cewa, kungiyar Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin mai alaka da al-Qaida ce ta yi garkuwa da mutanen uku.

Karin labari: “Mun gano haramtattun matatun mai 84 cikin mako ɗaya” – NNPCL

Ba’a dai bayyana yadda aka kuɓutar da mutanen uku ba, amma rahoton ya ce jami’an tattara bayanan sirri na Italiya ne suka yi aikin kuɓutar da su ta hanyar tuntubar shugabannin yankin.

Ƙasar Mali dai na ƙoƙarin shawo kan rikicin da aka kwashe shekaru goma ana gwabzawa da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka kawo tarzoma a yankin, inda ‘yan bindiga ke amfani da ƙasar a matsayin wani shingen kaddamar da hare-hare a yankin Sahel.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here