Ministan Burtaniya zai gana da dangin wata ‘yar Kenya da aka kashe

Kenya, burtaniya, minista, kashe, charles, sarki
Ministan Sojin Birtaniya ya yi tayin ganawa da iyalan wata mata ‘yar Kenya da ake zargin wani sojan Birtaniya ne ya kashe ta fiye da shekaru goma da suka...

Ministan Sojin Birtaniya ya yi tayin ganawa da iyalan wata mata ‘yar Kenya da ake zargin wani sojan Birtaniya ne ya kashe ta fiye da shekaru goma da suka gabata.

James Heappey ya shaidawa BBC cewa kasancewar ya fahimci irin radadin da ‘yan uwan ​​Agnes Wanjiru ke ciki, wanda aka gano gawarta a shekara ta 2012 a cikin wani tanki mai ɗauke da ruwa a kusa da wani sansanin sojojin Birtaniya da ke Nanyuki a tsakiyar kasar Kenya.

Da yake magana da jaridar a wata ziyara da ya kai ƙasar, ya ce “Na fahimci radadin da suke ciki, zan yi farin cikin haduwa da tattaunawa da kuma fahimtar yadda za’a iya taimakawa iyalinta.”

Karin labari: An sako wasu ‘yan Italiya 3 da aka yi garkuwa da su a 2022 a Mali

A ziyarar da ya kai Kenya a baya, Heappey ya ba da shawarar ganawa tsakanin jami’an Burtaniya da dangin Wanjiru, amma ba’a samu ko daya ba.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne iyalanta suka rubuta budaddiyar wasiƙa zuwa ga Sarki Charles suna cewa “Da alama jami’an Birtaniya ba su damu game da ƴar su da aka kashe ba” in ji shi.

Ya kara da cewa kuma sun nemi sarkin ya kai masu ziyara a lokacin da yake tafiya kasar.

Karin labari: “Babu wanda zai rasa aikinsa lokacin haɗe hukumomin gwamnati” – Mohammed Idris

Shekaru bakwai bayan mutuwar Wanjiru, wani bincike da aka gudanar a Kenya ya tabbatar da cewa sojojin Birtaniya daya ko biyu ne suka kashe ta.

Bayan rahotannin da ake zargin an yi rufa-rufa ne, ma’aikatar binciken manyan laifuka ta Kenya ta buɗe wani bincike, amma har yanzu ba ta tuhumi kowa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here