Kamfanin MTN ya bayyana dalilan katsewar sadarwa

MTN, kamfani, sadarwa, dalilan, katsewa, bayyana
Hanyar sadarwar MTN ta lalace yayin da masu amfani da sabis na sadarwa ke ganin ba zai yiwu a yi kira ko karɓar kira ba, yayin da wasu ba sa iya amfani da...

Hanyar sadarwar MTN ta lalace yayin da masu amfani da sabis na sadarwa ke ganin ba zai yiwu a yi kira ko karɓar kira ba, yayin da wasu ba sa iya amfani da intanet ta hanyar sadarwar.

Wannan ya samo asali ne sakamakon ƙalubalen hanyar sadarwa.

Kamfanin na MTN, yayin da ya magantu kan hakan a daren Laraba ya bayyana dalilin matsalar sadarwar a matsayin “babban katsewar sabis sakamakon yanke fiber da yawa, har ya shafi ayyukan murya da bayanai.”

Karin labari: Ministan Burtaniya zai gana da dangin wata ‘yar Kenya da aka kashe

Hukumar sadarwar ta kara da cewa injiniyoyin na ta suna aiki tukuru don warwarewa tare da dawo da aiyukan a wasu wurare a hankali.

“Muna neman afuwar rashin jin daɗi kuma muna neman haƙuri da fahimtar ku yayin da kamfanin ke aiki don dawo da cikakken sabis da wuri-wuri,” in ji mai ba da hanyar sadarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here