
Kotun ƙolin Amurka ta amince ta yanke hukunci a kan ko za’a iya gurfanar da tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump a gaban shari’a a kan zargin yunƙurin soke zaɓen shugaban ƙasar na shekarar 2022.
Tuni dai kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da buƙatar da Mista Trump ya shigar a gabanta a kan cewa yana da rigar kariya a matsayinsa na shugaban ƙasa.
Karin labari: Kungiyar masu gidajen burodi sun janye yajin aiki a Najeriya
A wani labarin kuma wata kotu a New York a jiya Laraba ta ƙi amincewa da buƙatar Mista Trump ɗin ta jinkirta biyan tarar dala miliyan 450 don aikata zamba.
An dai gano cewa tsohon shugaban ƙasar Amurkan ya yi ƙarya game da darajar dukiyarsa domin kaucewa biyan haraji da inshorar lafiya.