Gwamnatin Koriya ta Kudu ta yi barazanar ɗaukan matakin shari’a a kan dubban likitocin da ke yajin aiki idan ba su koma bakin aiki ba a ƙarshen wannan rana ta Alhamis.
Ta kuma ce za ta dakatar da lasisin aikinsu.
Kusan kashi uku bisa huɗu na ƙananan likitocin ƙasar sun dakatar da ayyukansu a makon da ya gabata.
Karin labari: Kotu za ta yanke hukunci kan ko Trump na da kariya daga tuhuma
Likitocin dai na adawa ne da shirin gwamnatin ƙasar na ƙara yawan ɗaliban da ke karatun likitanci a kowace shekara.
Wakiliyar BBC ta ce likitocin na ganin cewa matakin ba zai shawo kan matsalar ƙarancin likitocin da ake fuskanta a yankunan karkara da kuma sashin ba da kulawar gaggawa ba.
Likitocin dai sun dage da cewa ya kamata a fara shawo kan kura-kuran da ke tsarin kiwon lafiyar ƙasar da suka haɗa da rashin biyansu albashi mai tsoka da kuma yanayin aiki.