YANZU-YANZU: PDP ta musanta bawa wata shiyya tikitin takarar shugaban kasa a 2023

6D8E209A 2552 424A A293 70648950A849
6D8E209A 2552 424A A293 70648950A849

Babbar Jam’iyyar adawa a Nigeria PDP ta ce ba har yanzu bata yanke shawara kan yin tsarin shiyoyi a yayin bayar da tikitin takarar shugaban kasa a 2023.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan yayin da yake watsi da wasu jita-jita.

“An janyo hankalin jam’iyyar PDP kan wasu bayanai da suka janyo ce-ce-ku-ce a sassa daban-daban na kasar nan kan yadda wasu mutane ke ikirarin cewa jam’iyyar bawa wani yanki tikitin tsayawa takarar shugaban kasa.

A cewar sanarwar PDP jam’iyyar siyasa ce da aka kafa ta bisa ka’idojin dimokuradiyya, kuma duk wani mataki na jam’iyyar da ya hada da shiyya-shiyya, ya dogara ne kan tuntuba mai yawa, tattaunawa da yin la’akari da dukkan batutuwa da kuma dabi’u da muradu daban-daban a fadin kasa, tare da babban makasudin tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da ci gaban al’ummarmu.

“Saboda haka PDP ta bukaci ‘yan Najeriya, da magoya bayanmu da su yi watsi da ikirarin shiyya-shiyya marasa tushe kamar yadda ake yi.

PDP ta godewa ‘yan Najeriya a fadin duniya saboda dimbin sha’awar da suke da ita a cikin jam’iyyar a matsayin tabbataccen tsarinsu na Ceto da Gina al’ummarmu daga rashin mulki tare da rokonsu da su kasance da hadin kai da mai da hankali yayin da muke hada karfi da karfe don aikin da ke gabanmu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here