Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Yar Najeriya Tobi Amusan murna, da ta lashe kyautar zinariya a gasar mita 100 ta tseren mata ta Duniya da ake gudanarwa a Amurka.
‘Yar wasan mai shekara 25 ta kafa tarihin ne a zagayen kusa da karshe inda ta kai layi cikin minti 12 da dakika 12.
Shugaban kasa ya taya murnanar ne a wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Mista Femi Adesina, ya fitar yau Litinin a Abuja.
Shugaban ya kuma yaba mata bisa kukarin da ta tayi na daga sunan Najeriya a idon duniya.












































