Harin Jirgin Kasa: Iyalan wandanda aka yi garkuwar da su, sun yiwa ma’aikatar sufuri ta tarrraya Tsinke

Train Attack Victims Family
Train Attack Victims Family

Iyalan wadanda masu garkuwa suka Sace a jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna sun yiwa ma’aikatar sufuri ta tarayya dake babban birnin taraiya Abuja Tsinke, bayan wani faifan Bidiyo da Yan bindigar suka saki.

Zanga-zangar iyalan wandanda aka yi garkuwar da su dai ta zo ne sa’o’i 24 bayan ‘yan bindigar da ke tsare da su, sun fitar da wani sabon faifan bidiyo inda aka gansu suna yi musu bulala da sanduna yayin da suke kuka da neman a taimaka musu.

Duk da cewa an sako wasu daga cikin fasinjojin jirgin bayan an biya kudin fansa, an ce mutane da dama da abin ya shafa na hannun ‘yan bindigar.
Jaridar Solacebase ta Turanci ta cika shekaru biyar

A cewar iyalan duk da garkuwa da iyalan su da aka yi, gwamnati ta yi shiru bata ce komai, duk da halin da yan uwan su ke ciki.

Inda suke kira ga gwamnatin tarayya da ta yi duk mai yuwuwa wajen ceto musu yan uwan su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here