Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Malam Nuhu Ribadu ya miƙa wa gwamnatin jihar Kaduna mutane 59 da jam’ian tsaro suka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane.
Mutanen sun haɗa da maza 24, mata 28, da yara 6 da aka ceto daga wurare daban-daban a jihar Kaduna inda ɗaya daga ciki ke asibiti domin samun kulawa.
Ribadu ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin dukkanin hukumomin tsaro karƙashin umurnin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Karin karatu: Najeriya ta ki amincewa da kudirin sake fasalin sashin zaman lafiya da tsaro na AU
Ya kuma jinjina wa gwamnatin Jihar Kaduna na aiki tare da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro domin magance rashin tsaro a jihar.
Da yake karɓar mutanen da aka ceto, shugaban ma’aikatan jihar Sani Kila, wanda ya wakilci gwamnan jihar Uba Sani ya gode wa mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro na ganin cewa dukkan wanda aka yi garkuwa da su sun koma ga iyalansu.