Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan wasu kudirori guda uku bayan majalisar dokokin jihar ta amince da su.
SolaceBase ta ruwaito cewa sabbin dokokin da aka kafa sun hada da, dokar hukumar kula da sufuri ta jihar Kano (da ka yiwa gyara) ta 2025, da dokar kula da cututtuka ta Jihar Kano ta 2025 da dokar Kula da harkokin Tsaro ta jihar Kano ta 2025.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yau Talata, ta bayyana cewa gwamnan ya amince da kudirin ne a yayin da aka fara taron majalisar zartarwa ta jihar Kano karo na 25 da aka gudanar a gidan gwamnati.
A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ganin an samar da ribar dimokuradiyya da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar cikin hanzari.
Karanta: Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai sanya ido kan ayyukan kungiyoyi
Ya kuma jaddada cewa gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen bullo da manufofi da tsare-tsare da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya kuma nuna jin dadinsa da irin goyon baya da hadin kai da jama’a ke ba su, inda ya bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu domin cimma manufofin gwamnatin.
Rattaba hannu kan dokar da ke kula da tsaron unguwannin a jihar Kano ta 2025, na zuwa ne makonni biyu bayan majalisar dokokin jihar ta zartar da kudurin bayan tattaunawa mai zurfi.
Dokar, a cikin wasu tanade-tanade, ta bai wa jami’an tsaro ikon rike makamai, yaki da miyagun laifuka, kama mutane, da gudanar da ayyukansu a fadin jihar yayin da kuma ta ba da umarnin cewa wadanda ba su da alaka da siyasa ne kadai za a iya nada su shugabancin hukumar.