Ministan ci gaban harkokin ma’adinai, Dr. Dele Alake, ya amince da soke lasisin hakar ma’adinai guda 1,263 saboda masu lasisin sun gaza biyan kuɗin sabis na shekara-shekara.
Rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ce sanarwar ta fito ne daga mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Segun Tomori, a ranar Lahadi a birnin Abuja.
Wadannan lasisi da aka soke sun haɗa da lasisin bincike 584, lasisin hakar ma’adinai 65, lasisin ma’adinai na burbushin dutse 144, da kuma lasisin hakar ma’adinai kanana 470.
Ministan ya bayyana cewa matakin na cikin shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na tsaftace fannin ma’adinai.
Ya ƙara da cewa an cire waɗannan lasisi daga tsarin lantarki na Mining Cadastre Office (MCO) domin buɗe ƙarin damar saka hannun jari ga masu sha’awa.
Dr. Alake ya bayyana cewa biyan kuɗin sabis na shekara shi ne shaida mafi ƙanƙanta cewa mai lasisi na da niyyar hakar ma’adinai.
Ministan ya ce manufar gwamnati ita ce kawar da masu lasisin da ba sa aiki ko masu jiran sayar da damar ga mafiya ƙarfi, domin ba wa masu kishi da kuɗaɗe damar samun ingantattun wuraren hakar ma’adinai.
Ya yi gargadin cewa soke lasisin ba yana nufin an yafewa masu bashin kuɗin sabis ba, inda ya bayyana cewa jerin sunayen za a mika su ga hukumar EFCC domin tabbatar da biyan bashin ko kuma a gurfanar da su a gaban doka.
A cewar daraktan MCO, Simon Nkom, akwai masu lasisi 1,957 da aka fara gano basu biya kuɗin sabis ba, wanda ya sa aka wallafa sanarwar a jaridar gwamnati a ranar 19 ga Yuni, 2025 domin sanar da su su biya cikin kwanaki 30 kamar yadda dokar hakar ma’adinai ta 2007 ta tanada.
Tomori ya bayyana cewa jimillar lasisin da aka soke tun bayan zuwan gwamnatin Tinubu sun kai 3,794 ciki har da 619 da aka soke saboda rashin biyan kuɗin sabis da kuma 912 da aka soke saboda rashin aiki a bara.
A watan Agusta ministan ya sanar da niyyar soke lasisin fiye da 1,000 domin sake fasalin fannin ma’adinai, tare da samar da guraben aiki ga ’yan Najeriya da kuma tallafa wa masana’antu cikin gida.
Ya ce gwamnatin Tinubu na shimfiɗa harsashin Najeriya mai amfani da albarkatun ƙasa wajen samar da cigaba da bunƙasa arzikin ƙasa.













































