Kungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) reshen Jihar Kano ta kaddamar da sabbin shugabannin da aka zaɓa domin jagorantar harkokin ƙungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa.
Rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya bayyana cewa taron kaddamarwar ya gudana ne a babban taron shekara na ƙungiyar da aka gudanar a Kano, inda manyan dattawan Arewa suka halarta.
Cikin wadanda aka rantsar akwai Dr. Goni Faruk-Umar wanda aka sake zaɓa a matsayin Shugaba, Hajiya A’ishatu Maijama’a a matsayin Mataimakiyar Shugaba, Alhaji Abubakar Idris-Ahmad a matsayin Mataimakin Shugaba, da Dr. Aminu Usman-Jibrin a matsayin Sakataren ƙungiyar.
Haka kuma an kaddamar da sauran jami’ai ciki har da mataimakan sakatare da ma’aji, tare da kwamitin amintattu da ‘yan kwamitin.
Shugaban taron, Janar Haliru Akilu (rtd.), ya bayyana taron a matsayin wani babban mataki na sake jaddada aniyar ƙungiyar wajen bunƙasa haɗin kai, ingantaccen jagoranci da cigaban ƙasa.
Karanta: Gwamnatin Kano ta gargaɗi ƙungiyar tuntuɓa ACF kan sake kafa majalisar dattijai
Ya shawarci sabbin shugabanni da su ci gaba da gina kan nasarorin da suka gabata tare da ƙarfafa zaman lafiya, tattaunawa da muhimmancin siyasa da tattalin arziki ga yankin.
Shugaban kwamitin amintattu na ƙasa, Alhaji Bashir Mohammed-Dalhatu, ya yaba wa ƙoƙarin reshen Kano wajen yaki da talauci, ƙarfafa matasa da kuma shiga cikin kasuwanni da taruka.
Ya kuma ja hankalin sabbin shugabanni da su tabbatar da gina babban sakatari na dindindin, kammala littafin ACF reshen Kano, da kuma bayar da damar bunƙasa ga matasa 1,000 ta hanyar cibiyar horar da sana’o’in dogaro da Kai ta Akhuwat.
A nasa jawabin, babban sakatare na ƙasa na ACF, Alhaji Murtala Aliyu, ya tunatar da reshen jihohi cewa ba su da hurumin magana a madadin shugabancin ƙasa.
Duk da haka, ya tabbatar da cewa an magance matsalolin sadarwa da suka gabata, sannan ya yaba wa reshen Kano bisa irin nasarorin da suka samu tare da roƙon ƙarin jajircewa.
Shugaban da aka sake zaɓa, Dr. Goni Faruk-Umar, ya bayyana aniyar sabbin shugabannin wajen ƙara himma kan ayyukan da suka gabata da kuma faɗaɗa ayyukan ƙungiyar zuwa wajen birnin Kano.
Ya lissafa shirye-shiryen nan gaba ciki har da kammala littafin ACF Kano, gina sakatariya ta dindindin da kuma ƙirƙirar hanyoyin dogaro da kai ga matasa.
Haka kuma, tsohon kwamishinan kasuwanci da masana’antu na Kano, Alhaji Ahmad Rabiu, ya yaba wa ƙungiyar bisa jajircewarta, yana mai kira da su ƙara himma wajen yaki da talauci, rashin tsaro da sauran ƙalubalen tattalin arziki da suka addabi yankin Arewa.
NAN ta ruwaito cewa an bai wa mutane shida lambobin yabo, ciki har da kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) reshen Kano, Mr. Abubakar Idris-Ahmad, saboda gudunmawar sa wajen yaki da shaye-shaye.













































