Yan sanda sun gano matashiyar da ta bace daga Legas a Bauchi

Mildred Ebuka e 750x430 1
Mildred Ebuka e 750x430 1

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce an gano wata matashiya da ta bace a Legas a ranar Juma’a.

A cewar sanarwar da ‘yan sanda suka fitar, “Mildred Joshua Ebuka”, ‘yar shekara 17, ta bar gidansu da ke Victoria Island a birnin Legas tun ranar Alhamis don kai wa Yayar kawarta da ke Ikorodu hula.

A kan hanya ta hau motar bas kusa da gidanta.

Sai dai jami’an ‘yan sandan sun ce an same ta ne a Bauchi, inda suka sanar da iyayenta.

“Ta fito daga Legas kuma tana jin Turanci sosai. Sanye da riga da wando mara nauyi mai launin shudi, kuma ba ta da alamar kabila,” in ji rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi a wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunta Ahmed Mohammed Wakil.

A wani rubutu da rundunar ‘yan sandan Bauchi ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce an samu iyayenta.

“Muna matukar godiya ga ALLAH Madaukakin Sarki cewa rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta gano iyayen (Mildred Joshua Ebuka) Wanda ba sunanta ne na gaskiya ba, sunanta Jenifer Joshua Anga kuma a halin yanzu za a sadata da danginta cikin koshin lafiya. Na gode bisa hadin Kai da kishin kasa,” kamar yadda aka wallafa a shafin na Twitter.

Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels, mai magana da yawun ‘yan sandan, SP Wakil, ya ce iyayenta na kan hanyar zuwa Bauchi yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Ya ce an gano matashiyar ne a tashar mota, bayan da wani mutumin kirki ya mikata hannun ‘yan sanda sakamakon ta kasa gane inda take.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here