Sojoji sun kori jami’an da ake zargi sun kashe Sheikh Goni Aisami, tare da mikawa ‘Yan Sanda don gurfanar da su gaban Kuliya

Islamic Scholar in Yobe
Islamic Scholar in Yobe

Bataliya ta 241 ta rundunar sojojin kasar ta kori jami’anta John Gabriel da Lance Cpl Adamu Gideon, wandanda ake zargin sun kashe wani malamin addinin muslunci, Sheikh Goni Aisami a Yobe.

Babban Kwamandan bataliyar dake Nguru a jihar Yobe, Laftanal Kanal Ibrahim Osabo, ne ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan an yi nasarar kama wadanda ake zargin a Nguru.

Kamfanin Dillancin Labaran Kasa NAN ya rawaito cewa kafin sallamar jami’an da ake zargin sai da aka rage musu mukamansu daga mukamin Lance Corporal.
Ya kara da cewa za a mika wadanda ake zargin a hukumance ga hukumar ‘yan sandan kasar nan domin fuskantar shari’a.

“Mun kai su hedikwatar sashinmu da ke Damaturu, sannan Kwamandan sashin zai mika su ga rundunar ‘yan sanda a hukumance domin fuskantar shari’a.” in ji shi.

Kwamandan rundunar ya kuma yi Allah-wadai da abin da suka aikata kuma ya ce wannan ba hali ne na jami’an sojojin Najeriya.
“Ina so in tabbatar muku cewa mu ‘yan kasa ne masu bin doka da oda kuma a shirye muke mu yi adalci ga duk wanda aka samu da laifi, ba tare da la’akari da matsayi ko mukami ba,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here