Dan Leken asirin mayakan ISWAP a Rundunar Sojin Najeriya ya Kashe kansa bayan da aka kama shi

IMG 20220427 WA0381 666x381 1
IMG 20220427 WA0381 666x381 1

Wani sojan Najeriya da ke aiki a Bataliya ta Sojoji da ke Gaidam L/Kofural Jibril ya harbe kansa bayan da aka gano tare da kama shi da laifin hada baki da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP.

Wata majiya ta bayyana cewa al’amura sun fara sanya shakku game da sojan lokacin da ya bace daga wurin aikin sa na tsawon kwanaki biyu.

Majiyar ta bayyana cewa, a ranar 21 ga watan Afrilun 2022, an ga Sojan a cikin ‘yan ta’addan da suka kai hari a wata mashaya dake garin Gaidam tare da kashe mutane kusan 9.

Majiyar tace “A bisa haka ne, kwamandan sa, Laftanar Kanal Mikah, ya binciki wayarsa, aka gano shi a wani wuri a Gashua, cikin karamar hukumar Bade, mai tazarar daruruwan kilomita daga inda aka ajiye shi dan gudanar da aiki.

“An sake kai hari wata mashayar a Gashua, inda mutum daya ya mutu, wasu bakwai kuma suka jikkata, ana kyautata zaton Jibril na daya daga cikin wadanda suka kai harin,” in ji majiyar.

Ya bayyana cewa, nan take aka aika da sako zuwa sansanin Sojoji da ke Gashuwa tare da fadada bincike.

Da safiyar Talata ne Jibrin ya canza kama, ya shiga motar safe zuwa jihar Gombe, wanda akan hanya ne sojoji suka kama shi a shingen bincike da ke Gashua.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan an kama Jubril tare da daure shi da mari a hanyarsa ta zuwa Geidam, ya yi aiki da kwarewarsa a matsayin mai koyar da sarrafa makami, ya kwace bindiga daga hannun daya daga cikin masu rakiyarsa, ya ci karfin daya kuma ya tarwatsa kansa.

Abubuwan da suka bayyana lokacin da aka kama shi da tambayoyin da aka yi masa, sun kai ga kama wasu ‘yan’uwansa Cikin Sojojin masu aikata ta’addanci a boye.

Jibrin, dan Kabilar Babur wanda yake dan karamar hukumar Biu, yana cikin Hukumar Leken Asiri kafin ya zama malamin koyar da sarrafa makamai a rundunar ta soji.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here