Gwamnatin Tarayya ta horas da matasan Jihar Kano 177 akan gyaran manyan wayoyin zamani

FG trains 177 Kano youths on smart phone repairs – Minister 678x381 1
FG trains 177 Kano youths on smart phone repairs – Minister 678x381 1

Gwamnatin Tarayya ta horas da matasa 177 a Jihar Kano, kan yadda ake gyara wayoyin zamani, a wani bangare na gangamin samar da ayyukan yi ga matasa da kuma yaki da Fatara da talauci a tsakanin al’umma Najeriya.

Ministar Ma’aikatar kare afkuwar bala’i da jin kan al’umma ta kasa
Hajiya Sadiya Umar-Farouq, ce ta bayyana hakan lokacin da ake yaye matasan ranar Laraba a Kano.

Tace shirin N-Skill
She said that N-Skill shiri ne da ta gamsu da nagartarsa, la’akhari da yadda ake bada horon yadda ya kamata, kamar yadda ake yi Makaranta.

Sadiya Umar-Farouq, tace Gwamnatin Tarayya zata samar da duka kayayyakin aiki da ake bukata ga matasan da suka samu horon domin ci gaba da gudanar da sana’ar don tsira da mutuncinsu.

Sadiya Farouq ta kara da cewa wannan shirin da aka yi yanzu an yi shi ne a matsayin gwaji, kuma ya nuna irin jajurcewa da Gwamnatin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke yi wajen yaki da rashin ayyukan yi a tsakanin al’ummar Kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here