Alkali ya yi barazanar korar karar da Abba Kyari ya shigar kan danne hakkinsa

Abba Kyari new
Abba Kyari new

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Talata, ta yi barazanar yin watsi da karar da DCP Abba Kyari da aka dakatar, ya shigar da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA.

Mai shari’a Inyang Ekwo, ta ba da wannan gargadin ne biyo bayan jinkirin da lauya Kyari, Cynthia Ikena, ta yi, na bawa lauyan NDLEA, Joseph Sunday bayanai dangane da karar, duk da cewa an ba ta takardar shaidar karar tun ranar 28 ga watan Fabrairu.

A zaman da aka ci gaba da sauraren karar a ranar Lahadi, wani darakta mai kula da kararraki da shari’a na hukumar, ya sanar da cewa Ikena ya mika masa kara ne kawai a safiyar yau.

“An dage shari’ar ne domin sauraren muhimman hakkokin mai nema (Kyari). in ji shi.

Lauyan ya bayar da hujjar cewa ta hanyar tsari na 2 na Dokokin Hakkokin Hakkokin Bil Adama, 2019, mai nema bai samu lokacin shigar da bukatar ba.

Ikena, wadda ta yi korafin cewa sau uku tana yin kokarin ganawa da Kyari wanda ke tsare a hannun hukumar ta NDLEA, amma aka hana ta, ta bukaci a ba ta lokaci domin ta daidaita takardar.

Mai shari’a Ekwo, a wani takaitaccen hukunci da ya yanke, ya yi barazanar soke karar idan lauyan bata shirya ba daga nan zuwa gobe.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a ranar 21 ga watan Fabrairu ya ruwaito cewa Kyari, ta hannun Ikena, mika takardar neman a bi masa hakkinsa.

A cikin takardar, Kyari, wanda ya bayyana zargin da hukumar ta NDLEA ta yi masa a matsayin tada hankali, ya ce hukumar ta gaza tabbatar da lefin da taje zaginsa da aikatawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here