Asusun tallafi na NYSC zai taimaka wajen fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci – DG

NYSC Caps
NYSC Caps

Hukumar yi wa kasa hidima (NYSC), ta ce shirin bayar da tallafin zai taimaka wajen aiwatar da manufofin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na fitar da miliyoyin ‘yan Najeriya daga kangin talauci.

Babban Darakta Janar na NYSC, Manjo Janar. Shuaibu Ibrahim, ya bayyana haka ne a wajen bikin rufe shirin “A” Stream 1’ na shekarar 2022, ranar Talata a karamar hukumar Ganjuwa ta jihar Bauchi.

Ibrahim wanda Alhaji Namadi Abubakar, Ko’odinetan NYSC a jihar ya wakilta, ya ce za a yi hakan ne da zarar asusun ya fara aiki.

Shugaban NYSC ya kara da cewa da zaran Asusun Tallafawa ya fara aiki, za a kara inganta ingancin shirin koyar da sana’a na Skills Acquisition and Entrepreneurship (SAED).

Ya ce, za a cimma hakan ne ta hanyar samar da isassun kayayyakin horaswa da kuma samar da kwararrun masu horarwa.

“Yana da kyau ku sani cewa shirin SAED yana da tasiri sosai, don haka za’a bunkasa shi da zarar an kafa Asusun Tallafawa Matasa Masu Hidima na Kasa.

Ibrahim ya yabawa Majalisar Dokoki ta kasa bisa ci gaban da aka samu a kan harkokin dokoki kan kudirin kafa asusun.

“Ina so in yi kira ga hukumomin da suka dace da su yi gaggawar tabbatar da asusun ya fara aiki nan bada jimawa ba.

Shugaban NYSC ya bukaci masu hidimar kasa da su shiga cikin al’ummomin da suka karbi bakuncinsu, ta hanyar koyon harsuna da al’adunsu.

Ya kuma shawarce su da su ba da lokaci don gano bukatun al’ummomin tare da kaddamar da ayyukan ci gaban al’umma na kashin kansu da na kungiyance da za su daukaka matsayin rayuwarsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here