Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wadan da suka sami gurbin kartu a makarantun sakandaren Hadaka na Gwamnati

Adamu Adamu
Adamu Adamu

Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen wadan da suka sami gurbin karatu a makarantun sakadaren Hadaka na Gwamnati wato Unity College dake fadin Kasar nan guda 110, ciki har da Gifted Academy da ke Suleja.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi ta kasa, Mista Benjamin Goong ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Goon, ya shawarci iyayen da suka nemawa Yaran su guraben karatun a makarantun da su duba sunayen ‘ya ‘yan nasu a shafin ma’aikatar ilimi na Internet wato www.education.gov.ng.

Ya kuma ce zasu iya garzayawa makarantun da suka nema do min duba sunayen.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here