JAMB na shirin hukunta Cibiyoyin CBT da ke karya doka

JAMB new

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga makarantun gaba da Sakandare JAMB, ta bayar da shawarar hukunta cibiyoyi 11 na rubuta jarrabawar ta Kwamfuta watau CBT waɗanda aka samu da laifin saɓa ƙa’idojin jarrabawar a bana.

Shugaban hukumar ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan tafka maguɗi a jarrabawar wanda aka gudanar a Abuja yau Talata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, an kuma ba da shawarar hukunta masu cibiyoyin na CBT da ke da hannu a matsalar da aka samu ta shaidar yatsa yayin rajistar ta UTME.

Oloyede, ya ce hukuncin wanda har yanzu yana buƙatar amincewar Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ana son ɗaukarsa ne don kare mutuncin tsarin jarabawar. “Shugabannin JAMB da sauran masu ruwa da tsaki sun ba da shawarar cewa duk wata cibiyar yin rajista da ta yi rajistar mutane Kuma aka samu sama da 50 sun aikata laifuffuka za a hana su shiga duk wani aiki na Hukumar.

“Bayan dakatarwar da aka yi na tsawon shekaru uku, hukumar za ta sake duba ta, ta duba batun, idan wanda aka samu da laifi ya nuna nadama, za a iya janye dakatarwar.

“Sauran wadanda suka yi rajista kasa da 50 za a yi musu gargadi, kuma za a bukaci su rubuta wasikar neman yafiya ga hukumar bayan sun bayar da takardar shaida, wadda ke nuna cewa ba za su sake shiga irin wannan abu ba,” inji shi.

Oloyede ya kara da cewa an gargadi dukkan cibiyoyin CBT da ke da hannu a cikin keta doka su sanya hannu tare da bayar da shaidar horar da masu rajista.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here