ASUU ta yi watsi da tayin tallafin kudi domin ta janye yajin aikin da take yi

70d36724d8c940b4bbca437e0dc01727
70d36724d8c940b4bbca437e0dc01727

Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU, ta yi fatakali da tayin da aka yi mata na tallafin kude domin ta janye yakin aikin da ta tsondoma.

Shugabannin kungiyaar ta ASUU sun ki Amin cewa da jama’a su yi karo-karon kude domin biya wa kungiyar bukatun da suka sa ta shiga yajin aiki ne bayan an yi musu tayin hakan a safiyar ranar Asabar.

Hakan ya taso ne a lokacin da aka karbi bakuncin kungiyar a shahararren shirin Brekete Family wanda gidan rediyon Human Rights ke gabatarwa a Abuja.

Shirin ya gayyato Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke da jami’an kungiyar ne domin su yi wa ’yan Najeriya bayanin dalilin yajin aikin da ya ki ci, ya ki cinyewa.

Gabanin haka, shahararren mai gabatar da shirin, Ahmed Isah, ya kafa asusun tara wa kungiyar kudade domin share mata hawaye ta janye yajin aiki.

A lokacin tattaunawar ta ranar Asabar, Ahmed Isah, ya gabatar da Naira miliyan 50 da Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Udom Emmanuel, ya bayar domin sanyawa a asusun tallafin da aka bude a bankin TAJ.

Nuna kudaden ke da wuya, shugaban kungiyar ya nesanta kungiyar da kudaden da ake tarawa.

A kan haka ne Ahmed Isah ya yi barazanar dakatar da gidauniyar tunda kungiyar ba ta bukata.

Yawancin wadan da suka kira shirin ta waya dai sun bayyana furucin na ASUU a matsayin rashin sanin ya kamata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here