Kotun ma’aikata ta kasa yau Laraba ta umarci malaman jami’oi’in Najeriya dasu kuma bakin aiki ba tare da bata lokaci.
A ranar Litinin ne lauya mai kare gwamnatin tarayya, ames Igwe , ya roki kotun da ta tilastawa ASUU komawa bakin aiki, duba da illar da yajin aikin yake haifarwa.
Igwe ya ce doba da dokokin ma’aikata, kotu nada ikon tilasatwa ASUU komawa bakin aiki ya yin da tau taunawa ke cigaba da gadana.
Sai dai lauya mai kare kungiyar ta ASUU, Femi Falana, ya ce gwamnatin tarraya dole ta fara bayyana illar da yajin aikin ya haifar kafin kotun ta tilasta komawa bakin aiki.
Ya yin da yake yanke hukunci, mai shara’a Polycarp Hamman, ya ce yanke hukuncin ya zama dole domin batu ne na muradan kasa da kuma ‘yancin da dalibai suke dashi na a basu ilimi kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin Najeriya.













































