Shekarau ya Bayyana Ficewarsa daga NNPP zuwa PDP a zauren Majalisar Dattawa.

Sanatan Kano ta tsakiya Ibrahim Shekarau, ya bayyana ficewar sa daga jam’iyyar NNPP, zuwa PDP.

Shekarau, ya bayyana komawar tasa Jam’iyyar PDP ne ranar Laraba a zauren majalisar Dattawa.

Tun a ranar 29 ga watan Agustan da ya gabata ne Shekarau ya sauya sheka tare da magoya bayansa zuwa PDP, kan batutuwan da suka shafi rashin adalci da shugabancin jam’iyyar ta NNPP ke yi.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, shi ne ya karanta wasikar inda ya bayyana sauya shekar a hukumance.

Shekarau, a cikin wasikar ya ce ficewar sa da dubban magoya bayansa da suka yi a Kano daga NNPP zuwa PDP, sun yi ne don tabbatar da burinsu na siyasa a jam’iyyar da ta dace da su.

Bayan sanarwar, Sanatocin PDP karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Philip Aduda, Chukwuka Utazi sun yi maraba da sauya shekar Shakarau din zuwa jam’iyyarsu ta PDP.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here