Hukumar Ilimi a matakin farko ta tarayya ta ce za ta gina makarantun koyon aikin tattara bayanai da sadarwa na zamani guda shida a shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida akan kudi Naira biliyan 3 da miliyan 6.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar ta UBEC ta fitar a Abuja ranar Laraba mai dauke da sa hannun Jami’in hulda da jama’a na hukumar, David Apeh.
“Jami’an hukumar sun kuma fara kokarin tabbatarwa tare da aiwatar da shirye-shiryen koyo da koyarwa ta kafar Internet a fannin ilmi a fadin kasar nan, biyo bayan kalubalen da aka samu a bangaren dokar kullen COVID-19 da aka rufe makarantu.” ‘
Sanarwar ta ce “Hukumar tana gina makarantun guda shida (wato makarantun koyon fasahar sadarwar zamani) a shiyyoyin siyasar kasar guda shida akan kudi kusan Naira biliyan 3 da miliyan 6 karkashin shirin tsarin ilimin ta kafar Internet wato e-Learning a kasar.’’
“Kazalika UBEC tana fatan gina irin wadannan makarantu a dukkan jihohin kasar nan 36, inda aka kiyasta kudin kowannensu zai kai kusan Naira miliyan 350.
“Makarantun za su sami damar daukar dalibai da yawa kuma za a zuba kayan aiki na zamani.”
A cikin sanarwar, Sakataren zartarwar hukumar ta UBEC, Dakta Hamid Bobboyi, ya ce, “Kalubalen da aka fuskanta a bangaren ilimi na baya-bayan nan, wanda annobar cutar Covid-19 ta haifar, ya kara habaka bukatar sabbin hanyoyin koyo da koyarwa da zasu baiwa masu koyo da malamai damar koyo da koyarwa cikin sauki; don haka muka yi tunanin samar da shirin e-learning cikin tsarin ilimi a matakin farko.
“Abin farin ciki, hukumar, tun kafin barkewar cutar ta Covid-19, ta himmatu matuka wajen aiwatar da muhimman ayyuka guda biyu; da Smart Schools da E-learning.
“A kan haka ne hukumar UBEC ta ke ba da shawarar gudanar da taron bita na kwanaki 5 don samar da manhaja don horar da masu lura da bangaren ilimi da Malamai da masu taimaka wa a bangaren fasaha da sauran masu ruwa da tsaki kan shirin na Smart School da kuma E-Learning. ”
A cewar sanarwar, Bobboyi ya kara da cewa horon zai shafi dukkan batutuwan da suka shafi yadda ake amfani da kayan aiki na Sadarwar zamani (ICT) daban-daban yadda ya kamata domin baiwa malaman damar amfani da su yadda ya kamata; yana mai cewa hakan zai kuma shafi bangarorin da ke da alaka da kunshin manhajoji daban-daban da kuma amfaninsu wajen koyarwa ta hanyar Intanet.
Akan koyar da ilimin zamani, shugaban UBEC ya ce hakan zai mayar da hankali ne wajen bunkasa fasahar malamai kan koyar da darusa ta kafar Internet, inda ya bayyana cewa dabarun koyar da ilimin da ake bukata domin isar da sako ta hanyar Internet ya sha bamban da dabarun ilmantarwa ido-da-ido.













































