Hukumar zabe ta kasa INEC ta ce ‘yan Najeriya miliyan ashirin ne basu karbi katin zabensu na din-din-din ba wanda tuni ya kammala.
Shugaban hukumar mai kula da birnin tarayya Abuja da jihohin Kaduna, Nasarawa da Filato, Muhammed Haruna ne ya bayyana haka jiya Talata, yayin da yake kaddamar da shirin wayar da kan jama’a domin karfafa musu gwiwa wajen ci gaba da yin rigistar katin tare da karbarsa.
Muhammad ya tabbatar da cewa kididdigar da INEC ta fitar a shekarar 2019 ta nuna cewa an buga katin zaben wanda ya kai kimanin miliyan tamanin da hudu, inda daga ciki aka karbi miliyan saba’in da biyu, sama da miyan 11 ke jibge a hukumar.
Ya kara da cewa al’ummar yankin Kudu maso Yammacin Najeriya ne ke da katin mafi yawa wanda ba’a karba ba, wanda ya kai adadin miliyan 3 da dubu dari hudu, sanan kuma Arewa Maso Yamma suke biye musu baya da miliyan 1 da dubu dari tara, sai kuma yankin Kudu maso Kudu da adadin nasu ya kai kimanin miliyan 1da dubu dari bakwai.
Yayin da Arewa ta tsakiya ke da miliyan daya da rabi sai kuma Kudu maso Gabas miliyan 1 da dubu dari hudu, yayin da yankin Arewa masu gabas ke da katin kimanin guda dubu dari twas wanda ba a karba ba sai birnin ta raiya Abuja mai kimanin dubu dari uku da goma sha takwas.













































