A yayin jawabin na shugaban ƙasar, ya soma ne da bayani kan muhimmancin ranar dimokraɗiyya inda ya jaddada muhimmancin zaɓen Yunin 1993 a tarihin Najeriya.
Shugaba Buhari ya ce kada ƴan Najeriya su manta da irin gudunmawa da sadaukar da kai da gawarazan dimokraɗiyya suka bayar a 1993. Ya buƙaci ƴan Najeriyar da su yi koyi da kishin ƙasa irin na magabata a duk lokacin da za su zaɓi shugabanin.
Shugaban ya sake tuna wa ƴan Najeriya cewa wannan ce ranar dimokraɗiyya ta ƙarshe da zai yi a matsayinsa na shugaban ƙasa inda ya ce yana cike da ƙudirin tabbatar da cewa an zaɓi sabon shugaban ƙasa ta hanyar zaɓen gaskiya da adalci.
Haka kuma shugaban ƙasar ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen fitar da gwani a ƙasar inda ya ce ɗaya daga cikin abin da ya birge shi da zaɓen shi ne yadda mata da matasa a kusan duka jam’iyyun suka fito neman takara inda ya ce wannan alama ce da ke nuna dimokraɗiyyar Najeriya ta ƙara bunƙasa a cikin shekara 23 da aka shafe.
Kan dai batun zaɓe, shugaban ya bayyana cewa a shekara bakwai da gwamnatinsa ta shafe kan mulki, gwamnatinsa ta yi ƙoƙari wurin gyara dokokin zaɓe da yanayin gudanar da zaɓen domin kare ƙuri’un.
Shugaban ya bayyana cewa ɓangaren zartarwa da dokoki da kuma shari’a na da kudirin ganin sun aiwatar da waɗannan sauye-sauye na dokokin zaɓe a yayin zaɓen 2023.













































