INEC ta ce har yanzu bata karbe sunan wani dan takarar gwamna ba a jihar Kano.
Shugaban hukumar zaben reshen jihar Kano, farfesa Riskuwa Arabu Shehu ya shaidawa jaridar Solacebase hakan ne a yau Litinin.
Farfesa Arabu ya ce har yanzu jam’iyyu ba su basu sunayen wadan da zasu yi musu takara ba.
A karshin satin da ya gabata ne dai aka tashi da labarin bayyanar ‘yan takarar gwamna biyu a jam’iyyar PDP, Muhammed Abacha da Sadik Wali, inda kowanan su ke ikirarin cewa hukumar INEC ta bashi shaidar shiga zabe.
Jam’iyyar PDP dai a Kano ta rabu gida biyu, tsagin Wada Sagagi wanda shi uwar jam’iyya ta kasa da kuma kuto suka sani, sai daya tsagin wanda Aminu Wali ke jagoranta.
“INEC ta je wajan zaben fitar-da-gwani da akayi na Muhammad Abach, amma hukumar bata halarci na Sadiq wali ba’’
Inda ya kara da cewa har yanzu akwai sauran wa’adi harzuwa 17 ga watan da muke ciki na shekarar 2022, da jam’iyyu zasu bawa hukumar INEC sunayen ‘yan takara da mataimakan su a fadin Najeriya,
”INEC ba ta karbar sunayen ‘yan takara ba tare da na mataimakan su ba’’













































