Karancin Man Jirgin Sama ya yi Kamari, Akwai yuwuwar dakatar da zirga-zirgar Jirgage – AON

AirlineS 2
AirlineS 2

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa (AON) tace akwai yiwuwar karancin man jirgin wato Jet-A1 da ya yi kamari zai iya shafar jadawalin tafiye-tafiye.

Mai magana da yawun hukumar ta AON, Farfesa Obiora Okonkwo, shi ne ya bayyaana hakan ta cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar ranar juma’a aka gabatar a Legas,
Ta cikin sanarwar Farfesa Obiora Okonkwo, ya yi kira ga jama’a da ke tafiye-tafiyen da su fahimce su.
Jaridar Solacebase ta Turanci ta cika shekaru biyar
“Wannan wani hasashe ne amma babu tabbaci kuma ba niyyar mu ba kenan, hakan ka iya faruwa ne sakamakon karancin man da ake fama da shi a kasar nan.

“Saboda haka, muna rokon jama’a tafiye-tafiyen da su yi hakuri da mambobinmu saboda a halin yanzu ana kokarin magance matsalar da kuma ci gaban da dawo da ayyukan jiragen sama kamar yadda aka saba.

“AON ta himmatu wajen gudanar da ayyukanta na zirga-zirgar jiragen sama a duk fadin kasar.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here