Rundunar ‘yan sanda a Neja ta kubutar da mutane tara da aka sace a kauyen Kuchi da ke karamar hukumar Munya a jihar.
Kwamishinan Yansandan Jihar Bala Kuryas, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai ranar juma’a a Minna babban birnin jihar.
Bala yace, tun a daren ranar alhamis ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da mutanen.
Kwamishinan ya kara da cewa yanzu haka dai wadanda aka yi kubutar din an sada su da iyalansu.
Ya kuma nemi karin goyon bayan mazauna yankin ta hanyar bawa rundunar sahihan bayanai da za su taimaka wajen kawar da miyagu a jihar.