Abba Kyari ya maka gwamnatin tarayya a gaban kotu

Abba Kyari
Abba Kyari

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda da aka dakatar, DCP, Abba Kyari ya maka gwamnatin tarayya a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja yana kalubalantar ci gaba da tsare shi da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ke yi.

Cikin wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22 Jami’in tsaron yana nemi kotu da ta bada umarnin gaggauta sakin shi.

Abba Kyari  ya shigar da karar ne ta hannun lauyansa, Mrs P. O. Ikenna, inda ya shaida wa kotun cewa ana tsare da shi “a kan zargin karya da aka yi masa”.

Duk da haka, lokacin da aka gabatar da karar, Mai shari’a Inyang Ekwo, ya lura cewa karar ta kunshi wasu abubuwan da za su bukaci martanin gwamnatin tarayya.

Kokarin da lauyan mai kara ya yi na jan kunnen kotun da ta ba da umarnin a saki Kyari saboda “lafiyarsa ta tabarbare”, ya ci tura.

A maimakon haka, Mai shari’a Ekwo ya ba da umarnin a bi dukkan matakan da suka dace wajen sanar da gwamnatin tarayya, domin bayyana a gaban kotun. Sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here