Matatar Man Dangote ta amince da mayar da ma’aikatan da ta kora

Dangote refinery

Rukunin kamfanonin Dangote ya amince da mayar da ma’aikatan da aka kora daga Matatar Man Fetur ta Dangote, tare da sake tura su zuwa wasu sassa na kamfanin.

Wannan mataki ya biyo bayan zaman sulhu da aka gudanar tsakanin bangarorin da abin ya shafa.

Ma’aikatar Kwadago da Ayyuka ta sanar da hakan a ranar Laraba, tana bayyana sakamakon zaman da aka yi a ranar Litinin da Talata.

A wajen zaman, shugaban kamfanin, Aliko Dangote, tare da shugabannin Kungiyar PENGASSAN sun gana da ministocin gwamnati, ciki har da Wale Edun, ministan kudi da mai kula da tattalin arzikin kasa, da kuma Mohammed Dingyadi, ministan kwadago da ayyuka, domin sasanta rikicin.

Sanarwar ta ce bangarorin sun amince cewa dukkan ma’aikatan da aka kora za a sake tura su zuwa wasu sassa na kamfanonin Dangote Dangote ba tare da sun yi asarar albashi ba.

Labari mai alaƙa: Gwamnatin tarayya, PENGASSAN da Dangote sun cimma yarjejeniya kan rikicin matatar mai

Haka kuma, ba za a hukunta kowanne daga cikin ma’aikatan da suka taka rawa a wannan rikici ba.

Ma’aikatar ta kara da cewa, an jaddada cewa ‘yancin kafa kungiyar kwadago hakki ne da dokokin Najeriya suka tanada, dole kuma a mutunta shi.

Haka nan, PENGASSAN ta amince ta fara matakan janye yajin aikin da ta kira.

A ranar 26 ga Satumba ne PENGASSAN ta umurci mambobinta da su shiga yajin aikin kasa baki daya, bayan kora da kamfanin man fetur na Dangote ya yi wa wasu daga cikin ma’aikatansa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here