Najeriya@65: Gwamna Yusuf ya bukaci shugaba Tinubu ya cire kwamishinan ƴan sandan Kano

WhatsApp Image 2025 10 01 at 12.14.10 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabiru Yusuf, ya roki Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya sauke kwamishinan ’yan sanda na jihar bisa zargin rashin iya aiki.

Gwamna Yusuf ya yi wannan kira ne a ranar Laraba yayin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Ya jaddada cewa ’yan Najeriya na bukatar jami’an tsaro masu gaskiya da adalci, wadanda za su kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba tare da son rai ko tasirin siyasa ba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa wannan bukata ta samo asali ne daga janye jami’an ’yan sanda a yayin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai a Kano.

Gwamnan ya bayyana wannan mataki a matsayin “abin kunya kuma ba daidai ba,” yana mai cewa irin wannan hali na iya rage darajar hadin kai da alhakin kasa baki daya da bikin samun ’yancin kai ke wakilta.

A baya dai rahotanni sun nuna cewa dangantaka tsakanin gwamnatin jihar Kano da rundunar ’yan sanda ya yi tsamar tun daga 2023, inda aka fara da tsohon kwamishina Husaini Gumel, daga bisani Salman Dogo, sannan yanzu Bakori.

Cikakkun bayanai daga baya…

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here