Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kudaden Muhalli, wanda dan majalisa daga Jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji ke jagoranta, ya bayyana cewa Jihar Kano za ta amfana da tallafin kudaden muhalli domin magance matsalolin kwararowar kasa.
Jaji ya yi wannan bayani ne a ranar Talata a Kano yayin wata ziyara ta musamman da kwamitin ya kai domin ganin yadda matsalar zaizayar kasa ta yi kamari a wasu wurare a jihar, tare da rubuta rahoto don samar da dauki cikin gaggawa daga Gwamnatin Tarayya.
Jaji ya ce, “Mun ziyarci Jihar Kano kamar yadda muka ziyarci wasu jihohi domin ganin yanayin halin da wuraren da suka fuskanci zaizayar kasa ke ciki, da kuma irin matsalolin da wannan al’amari ke haifarwa, tare da daukar matakan gaggawa don taimakawa wuraren da abin ya shafa, sannan kuma mu tattara rahoto mai kyau domin a dauki mataki cikin sauri daga gwamnati.”
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kai na Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta Kano, Ismail Garba Gwammaja, ya fitar.
Jaji ya bayyana damuwa game da irin barnar da kwararowar kasa ke yi a wasu wuraren da abin ya shafa.
Duk da haka, ya nuna fatan cewa kwamitinsa zai yi duk mai yiwuwa ba tare da wani jinkiri ba domin tattara rahoto mai kyau da zai sa gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa.
Har ila yau, ya yabawa gwamnatin jihar da Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi musamman bisa jajircewarsu da kokarinsu na hana matsalar ta kara yaduwa zuwa wasu wurare.
A cewar sanarwar, Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar Kano, Hon. Nasiru Sule Garo, wanda ya zagaya da kwamitin Kudaden Muhalli na Majalisar Tarayya zuwa wuraren da aka samu matsalar kwararowar kasa, ya bayyana yadda kwararowar kasar ke lalata gonaki, hanyoyi, dukiyoyi, kuma wasu lokuta har da rasa rayuka.
Ya roki kwamitin da su dauki matakin da ya dace tun da sun ga halin da ake ciki da kansu don su mika rahoto da kimanta matsalar kwararowar kasa a Kano domin samar da daukin gaggawa.
SolaceBase ta ruwaito cewa wuraren da kwamitin ya ziyarta sun hada da wurin kwararowar kasa na Getso a Karamar Hukumar Gwarzo, Rarin a Dawakin Tofa, Bulbula Gayawa a Ungogo da kuma Kwankwasiyya a Karamar Hukumar Kumbotso.